Michel Barnier Ya Yi Murabus a Matsayin Firayim Ministan Faransa
Michel Barnier, wanda ya kasance Firayim Ministan Faransa, ya sanar da yin murabus daga mukaminsa. sanarwar murabus din ya Zo ne ba tare da wani cikakken bayani ba, amma ya ja hankalin 'yan siyasa da jama'a a Faransa da ma duniya baki daya.
Barnier, wanda ya shahara a fagen siyasa na Turai, musamman wajen jagorantar tattaunawar Brexit a matsayin wakilin Tarayyar Turai, ya bar matsayin nasa a wani lokaci mai mahimmanci ga gwamnatin Faransa.
Masana na ganin murabus dinsa na iya yin tasiri a siyasar cikin gida ta Faransa, musamman idan aka yi la'akari da kalubalen da gwamnatin ke fuskanta kan batutuwan tattalin arziki da zamantakewa. Ana sa ran za a nada wanda zai gaje shi nan bada jimawa ba domin ci gaba da tafiyar da ayyukan gwamnati.