Murtala Garo ga Baffa Babba Dan'agundi: Ka maida ni saniyar ware a APC

 Dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano a jam'iyyar APC, Murtala Sule Garo ya koka kan yadda ya ce kusa a jam'iyyar, Baffa Babba Dancing na maida shi saniyar ware.

A wani faifen bidiyo da ya karaɗe shafukan sadarwa, an ga Garo, a wajen wani taro da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya shirya a gidan sa na Kano, na nuna rashin jin dadin sa kan yadda Dan'agundi ke kin yabawa irin kokari da ya ke yi da jam'iyyar da kuma ƴaƴan ta a Kano.

A faiifen bidiyon, an gano Garo na nuna irin tiri-tiri da ya ke yi da ƴan jam'iyya duk da bashi da wani muƙami, inda ya kara da cewa duk da haka yana kokarin rike yan jam'iyyar domin tabbatar da hadin kai.

Ya kara da cewa, baya jin dadin yadda idan Dan'agundi ya na lissafo wadanda su ke yi wa jam'iyyar hidima ba ya lissafa wa da shi.

"Mu tarbiyyar mu ce tun ta iyaye da kakanni cewa idan za mu yi alheri ba sai mun baiyana ba, amma su wadanda muke musu sun sani,x in ji shi.

Haka dai, cikin raha, Garo ya miƙa sakon rashin jin dadin sa ga Dan'agundi, har sai da shugaban Jam'iyyar na jiha, Abdullahi Abbas ya karɓe abun magana daga hannun sa.

@Daily Nigeria Hausa 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org