Ƴar Jagoran Kwankwasiyya Rabiu Musa Kwankwaso ta zama mafi ƙwazo a ɓangaren Likitanci a Jami'ar Nile Abuja

Ƴar jagoran ɗarikar Kwankwasiyya, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ta zama mafi ƙwazo a ɓangaren Likitanci a Jami'ar Nile dake birnin Tarayya Abuja.

Madogara TV/Radio ta labarto cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da shugaban ɗarikar kuma mahaifin Aisha ya wallafa a sahihin shafinsa ma Facebook.

Kwankwaso ya bayyana cewa; "cikin karramawa na sake kasancewa da iyalina da ƴan uwa da bokan arziki a Jami’ar Nile ta Nijeriya da ke Abuja domin taya ‘yarmu Aisha Rabi’u Kwankwaso murna bisa gagarumar nasarar da ta samu a matsayin ɗaliba mafi ƙwazo da ta kammala karatun digirinta na farko a fannin likitanci". 

Sanarwar ta ci gaba da cewa; "Ta sami sakamako mafi kyau a ɓangarorin fannin ilimin halittar ɗan adam, kimiyyar halittu, ilimin halittar ɗan adam, likitancin yara, da kuma likitancin al'umma, kuma an karrama ta da wannan ƙwazon a wajen bikin shaidar da jami'ar ta shirya.

"Ina taya Aisha da mijinta Fahad murna tare da sauran ’yan uwanta waɗanda suka kammala karatunsu bisa wannan gagarumin ci gaba da suka samu, kuma ina musu fatan alheri a nan gaba", ya ƙarƙare.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org