'Na gaji, na yi iya yi na', Tiwa Savage ma duba yiwuwar yin ritaya daga waƙa
Shahararriyar mawakiyar Nijeriya ɗin nan Tiwa ta ce ta na tunanin yin ritaya bayan ta fitar da sabon kundin waƙoƙin ta nan gaba kadan.
A wani sako da ta wallafa a shafin ta na Instagram a yau Asabar, Savage, Mai shekaru 44 ta ce "Na gaji, na yi iya yi na", inda hakan kf nuni da cewa ta na son yin ritaya.
Sai dai ba ta fadi sunan sabon kundin waƙoƙin ba da kuma lokacin da za ta kaddamar da shi.