Na godewa gwamna Abba da ya gwale masu neman ya tsaya da ƙafar sa - Kwankwaso

 Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce ya na godewa gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar, da ya cewa masu cewa ya tsaya da ƙafar sa "ahir din ku".

Kwankwaso ya fadi hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa da aka watsa ta a yau Litinin.

Tsohon gwamnan na Kano ya kuma nuna rashin jin daɗinsa da yadda wasu ke neman haifar da ɓaraka tsakaninsa da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, biyo bayan wata sara da aka fito da ita a baya bayan nan mai taken (Abba Tsaya Da Ƙafarka), wadda ke neman gwamnan ya yi wa mai gidan na sa bar'a, ya raba gari da shi, saboda zargin ya kankane al'amuran gwamnati, ya hana ruwa gudu.


''Abun da mutane ba su gane ba shi ne mu fa Kwankwasiyya ƙungiya ce ba jama'iyya ba, mutane ne suka amince da mu, don haka idan gwamna ko wani dan majalisa da muka saka ya zo yana abun da ba shi ake so ba, ba wai sunansa kaɗai za a faɗa ba, cewa za a yi Kwankwasiyya ta gaza'' in ji Kwankwaso.

Ya ce babu ƙanshin gaskiya a zargin da ake yi masa na cewa yana shiga sharafin gwamnati har ya ce ga yadda za a yi, inda ya ce tun farko ya ce zai rika bayar da shawara ne idan an nema, kuma abun da yake yi yanzu ma kenan, kuma shawarar ma sai an nema.

A cewar Kwankwaso, masu neman Abba ya tsaya da kafarsa, mutane ne da ke da wata manufa ta siyasa, da suke ganin idan sun raba su, za su samu wata kofa da za su cimma manufarsu.

'Wasu fitinannun gani suke idan ya tsaya da ƙafarsa ya bar Kwankwasiyya, ba mamaki akwai masu neman gwamna a cikinsu, so suke idan ya yi kuskure sai su hada da mu da shi gaba daya su cimma manufarsu, don haka ina so in godewa shi gwamna, dama da shi suke, to ya fito ya ce ahir'' in ji Kwankwaso.

@Daily Nigeria Hausa 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org