Najeriya Da Faransa Sun Kulla Yarjejeniya Don hakar Ma’adanai A Najeriya

 Najeriya da Faransa sun cimma yarjejeniya kan aiwatar da ayyuka tare domin inganta harkar ma’adinai masu muhimmanci da fadada darajar bangaren ma’adinan da suke da amfani ga tattalin arzikin ƙasashen biyu.

Kamar yadda Ministan Ma'adanai Dela Alake ya bayyana a Shafinsa na X. 

"Mun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MOU) don karfafa hadin gwiwa wajen bincike, "Daya daga cikin manyan ginshikan wannan yarjejeniya shi ne kudurinmu na tallafawa hakar ma’adinai da zai dore, ta hanyar aiwatar da shirye-shirye da zasu rage illar muhalli, kamar hayakin carbon, yawan amfani da ruwa, da matsalolin dumamar yanayi.  

Haka zalika, yarjejeniyar ta kunshi shirin samar da hadin gwiwa wajen hako da sarrafa ma’adinai, tare da samun tallafi daga gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu. 

Wannan zai taimaka wajen inganta samar da ma’adinai da rage dogaro ga makamashi mai gurbata muhalli.



Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org