Najeriya Ta Samu Matukiyar Jirgin Sojan Ruwa Mace Ta Farko

 Laftanar Changfe Maigari ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko da ta zama matukiyar jirgi a rundunar sojojin ruwan Najeriya NN tun kafuwarta a shekarar 1964

Maigari, wanda ta ke da aure da kuma diya mace, ta fito ne daga karamar hukumar Langtang ta Arewa a jihar Filato amma an haife ta a jihar Kaduna.

Tafiyar ta ta ban mamaki ta fara ne a shekarar 2016 a lokacin da ta kammala karatunta a Kwalejin Tsaro ta Najeriya (NDA) kuma aka ba ta mukamin Sub Laftanar.

Daga baya, ta yi aiki a cikin Rundunar Sojojin Ruwa ta Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na Nakeriya NAN ya rawaito cewa an bai wa Maigari lambar yabo ta ‘Pilot Wing’ a lokacin bikin Sunset na shekrar 2024 NN a hedikwatar horar da sojojin ruwa, HQ NAVTRAC a Ebube-Eleme, Rivers, a ranar Juma’a.

A zantawarta da NAN a gefen taron, Maigari ta bayyana cewa ta cimma wannan matsayi ne bayan ta kammala horon na matukiyar jirgi da kuma cika dukkan bukatunta.

“Na taso ne a wurin aikin soja a lokacin da mahaifina jami’i ne a rundunar sojojin saman Najeriya.


"Tun ina karama ina burin zama matukiyar jirgin soja kuma lokacin da damar shiga sojan ruwa ta samu, ban yi kasa a gwiwa ba."

Ta ba da labarin yadda burinta na zama jami’ar sojan ruwa ya cika lokacin da aka zaɓe ta cikin rukunin farko na mata 20 da aka horar da su a NDA.

Maigari ta ce ta kammala karatunta a shekarar 2016 a matsayin babbar jami’ar koyon karatu, ta samu lambar yabo ta sojojin ruwa ta zinare, kuma a shekarar 2019 ta kammala karatunta na Sub Lieutenant Technical Course a matsayin mafi kyawun gabaɗaya.

“Akwai lokacin horo na da kamar ba zan yi nasara ba a karatuna ko tsarin jirgin sama, amma na daure.

"ZAMA mace ta farko matukiyar jirgi a Rundunar Sojan Ruwa ta Najeriya na ji da gaske da kuma wani gagarumin ci gaba, ba a gare ni kadai ba har ma ga dukkan abokan aikina mata wadanda za su iya samun kwarin gwiwa daga wannan nasarar.

“Ina kuma fatan nasarar da na samu ta zaburar da matasan farar hula ‘yan mata masu burin shiga aikin soja, musamman sojojin ruwan Najeriya, dagewa domin jajircewa na iya shawo kan duk wani kalubale a rayuwa,” in ji Maigari.

Sannan ta bayyana godiya ga Allah da abokan aikinta da kuma iyalanta bisa goyon bayan da suka ba ta wajen ganin ta samu nasarar zama mace ta farko da ta zama matukiyar jirgi a rundunar sojojin ruwan Najeriya.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org