Najeriya taza haɗa kai da Pakistan domin haɓɓaka noman zamani

 Gwamnatin tarayya ta sanar da shirinta na hada kai da gwamnatin kasar Pakistan domin habaka shirin samar da wadataccen abinci  a kasa.

Karamin minista a ma’aikatar gona ta tarayya Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ne ya tabbatar da hakan a karshen makon jiya a birnin Abuja lokacin da yake karbar bakuncin jakadan Pakistan a Najeriya Major Janaral mai ritaya Sohali Khan.

Ministan ya jaddada muhimmancin karfafa alaka a bangaren aikin gona a tsakanin kasashen biyu, inda ya ce, da jimawa Najeriya ke da dangantaka ta kut da kut da kasar Pakistan a sauran bangarorin ci gaba da suka hadar da al’adu.

Da yake jawabi, jakadan kasar ta Pakistan a Najeriya ya ce, kasar Pakistan tana da kwarewa sosai a bangaren fasahar zamani a kan aikin gona da kuma harkokin bincike a kan bangaren noma, inda ya yi fatan cewa alakar da za a kulla za ta kunshi baiwa kwararru a Najeriya damar ziyartar kasar ta Pakistan domin kara samun kwarewa sosai

Jaridar Nigeria.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org