"Nayi matukar mamaki da ganin jawabin mawaki da rigar masu fashin baki "_-Inji- Barrah Almadany.
A hakikanin gaskiya ya kamata makusantan Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya kamata su zaunar da shi su bashi shawara.
Domin shiga rigar masu sharhi ko fashin baki ba tashi bane ya tsaya a matsayinsa na mawaki mai neman na goro, shiga musayar yawu tsakanin Nijar da Najeriya ba tashi bane.
Domin sha'ani na kasa da kasa ba kowa ake buƙatar ya tsoma baki ba, dole sai mutanen da abin ya shafa don kawo daidaito da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu.
Mu yan arewa ne kuma yan Najeriya, ba alheri bane a gare mu ace yau na sami matsala tsakanin Najeriya da Nijar.
Ko babu dangantaka ta jini tsakanin mutanen Najeriya da Nijar, akwai alaƙa ta makwabtaka da harkar kusuwanci tsakanin kasashen biyu.
Babban hakkin dake kan mu shine samar da hanyoyin samar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu ba tare da fusata wani bangare ba.
kalaman Dauda Kahutu Rarara akan Shugaban sojin Nijar akwai rashin ilimi da wayewa a ciki.
Inji Matashi mai sharhi akan sha'anin Rayuwa Barrah Almadany.
@Karaduwa post Hausa