NCC ta ƙaryata rahoton ƙarin kudin kiran waya da na data
Hukumar Sadarwa ta Ƙasa, NCC, ta ƙaryata raɗe-raɗin da ke ta yi cewa kamfanunuwan waya za su yi karin kuɗin kira da na data daga watan Janairun 2025.
Wani babban ma'aikaci a hukumar ya shaidawa jaridar Vanguard cewa rahoton ba shi da tushe balle makama.
Ya yi bayanin cewa kamfanunuwan sadarwa ba sa yin ƙarin kudi ko daukar wasu matakai ba tare da biyayya ga dokokin sadarwa na ƙasa, NCA, waɗanda su ka ƙunshi tuntubar da bin ƙa'idoji kafin ɗaukar wani mataki, musamman na ƙarin farashi.