NDLEA ta bankado gonar tabar wiwi mai girman hekta 6 a Ogun

 Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), reshen jihar Ogun, ta yi nasarar lalata gonar tabar wiwi mai girman hekta shida da ke kauyen Alaka a jihar Ogun.

Shugaban hukumar a jihar, Mista Tijani Rabe, ya bayyana wannan nasara yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abeokuta a ranar Alhamis, inda ya gabatar da rahoton ayyukan hukumar na shekarar 2024.

Rabe ya ce an kama mutane hudu da ake bincika dangane da aikin gonar tabar wiwin.

Ya kuma bayyana cewa hukumar ta samu nasarori da dama a kokarinta na rage yaduwar fataucin miyagun kwayoyi.

A cewarsa, hukumar ta kama masu laifi 675 da ke da alaka da miyagun kwayoyi tare da kwace tan 9.7 da kuma lita 537.81 na miyagun kwayoyi masu ruwa.

Ya kara da cewa, a cikin wata sabuwar atisaye da ake kira “Operation Closed Gates” a watan Nuwamba, an kama wani mutum tare da buhunan tabar wiwi 100 masu nauyin tan 1.3.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org