Ni ban san Gowon ya Roƙi Tsohon Shugaban Kasa, Abacha kar ya Kashe ni ba - Obasanjo

 Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce bai taba sanin cewar tsohon mai gidan shi Janar Yakubu Gowon ya rubutawa Janar Sani Abacha wasika inda yake rokon shi a kan cewar kar ya kashe shi ba.

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo wanda ke mayar da martani a kan ikrarin Janar Gowon dangane da rubuta wasikar yace da ya san da haka da yaje ya gode masa lokacin da ya fita daga gidan yari.

Obasanjo yace bayan sakinsa ya ziyarci mutane da dama a ciki da wajen Najeriya yana musu godiya akan gudumawar da suka bayar wajen kubutar da shi, amma bai je wurin Janar Gowon ba saboda ba shi da labari a kai, sai jiya da ya yi magana a kai.

Saboda haka Obasanjo ya godewa tsohon mai gidan na sa da kuma duk wadanda suka bada gudumawa wajen ceto rayuwarsa daga hannun Abacha.

Gowon da Obasanjo sun yi wadannan kalamai ne a wajen bikin addu'oin Kirsimeti da gwamnatin jihar Filato ta shirya.

Obasanjo da Murtala suka kifar da gwamnatin Janar Gowon a shekarar 1975.


📷Caleb Mutfwang

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org