Olivia Hussey, tauraruwa a cikin fim ɗin ‘Romeo and Juliet’ ta mutu ta na da shekaru 73

 Olivia Hussey, shahararriyar jaruma wacce  ta burge duniya a matsayin Juliet a cikin shahararren fim ɗin Franco Zeffirelli na shekarar 1968, ta mutu tana da shekaru 73.

Iyalanta sun sanar da labarin mutuwar ta a shafin Instagram.

"Da baƙin ciki mai zurfi muke sanar da rasuwar Olivia Hussey Eisley, wadda ta rasu  a gidanta  a ranar 27 ga Disamba. Olivia ta kasance mace gwarzuwa wadda dumin zuciyarta, hikimarta, da kyautatawarta su ka shafi rayuwar duk wanda ya santa."

Rolin Hussey a cikin fim ɗin Romeo and Juliet, wanda ta yi tana da shekaru 15 kacal, ya bata lambar yabo ta Golden Globe a matsayin "Sabuwar Tauraruwa ta Shekara" kuma ya tabbatar da matsayinta a tarihin fina-finai.

@Daily Nigeria Hausa 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org