PSC ta karawa manyan ƴansanda 8,053 girma

 Hukumar Kula da Aikin ‘Yansanda (PSC) ta daga mukamin manyan ‘yansanda 8,053 zuwa matakai daban-daban.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Ani, ya ce an daga darajar Superintendents na ‘yan sanda guda 1,348 zuwa mukamin Chief Superintendent.

Ani ya kara da cewa, an daga mukamin Deputy Superintendents guda 876 zuwa Superintendent, yayin da Assistant Superintendents 5,829 aka daga zuwa mukamin Deputy Superintendents.

Ya bayyana cewa an amince da wannan karin girma ne bayan da hukumar ta kammala tantance shawarwarin da kwamitin da ke kula da karin girma ya gabatar.

Kwamitin, wanda mataimakin babban sifeton ‘yansanda, Taiwo Lakanu, yake jagoranta, shi ne ya tsara shawarwarin karin girman.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org