Rahotanni daga fadar sarkin Kano Malam Sunusi Lamido Sunusi dake kofar kudu na cewa jami'an tsaro sunyiwa gidan kawanya yanzu haka.
Yanzu Yanzu: Jami'an tsaro sun yi kawanya a kofar kudu, kofar shiga gidan sarkin Kano
Rahotanni da ke shigo mana sun ce a yanzu haka an sami ci koson ababan hawa a tintin kofar kudu zuwa kofar Nasarawa bayan da jami'an tsaro suka yi kawanya a harabar fadar sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi II.
A yau juma'a ne sarkin ya shirya yiwa hakimin Bichi rakiya zuwa fadarsa bayan nada shi da yayi, wanda wasu ke ganin jibge jami'an tsaron na da nasaba da fitar da sarkin zaiyi zuwa garin Bichi.
Aikin gadar da gwamnatin Kano ke yi a Kofar Dan Agundi ya tilasta wa masu ababen hawa yin ratse ta Kofar Kudu, sai dai wannan abu da ya taso a yau juma'a na cinkoso a gidan Sarkin ya jefa masu ababen hawa da ke ratse ta hanyar cikin halin kunci.
@AID Multimedia Hausa