Rai Bakwan Duniya Miji da mata sun rasa ransu cikin dare A Jihar Kano
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar miji da mata sakamakon tashin gobara cikin dare a gidansu da ke yankin Rangaza a ƙaramar hukumar Ungoggo ta Jihar.
Babban Daraktan hukumar na jihar, Hassan Muhammad ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Saminu Abdullahi, ya fitar ranar Juma'a a Kano.
A cewar sa, gobarar ta tashi cikin daren Alhamis ne, inda ta kone mutumin mai suna Muhammad Uba dan shekara 67 da matarsa Fatima mai shekara 52.
DCL Hausa