Rikici ya barke tsakanin motocin Gombe Line da Kaduna Line inda har ta kai ga yan Kaduna sun kwashe motocin Gombe Line dake tashar Unguwar Sarki

 Rahotannin sassafe daga Jihar Kaduna sun bayyana cewar an yi babu dadi tsakanin mahukunta Motocin Sufuri na Kaduna Line da na Gombe Line dake Lodi a Unguwar Sarki ta Jihar Kaduna.

Wannan ya biyo bayan tursasa wa tsagin Gombe Line dake lokadi a Unguwar Sarki kan dole sai sun koma Sabuwar tashar Lodi dake Lagos garradge Mando.

Kuma wannan turka-turkar ya biyo bayan samun fasinjoji masu yawa da Gombe Line suke yi sama Dana tsagin Kaduna Line.

Kamar a safiyar yau Juma'a sai da mahunta Kaduna Line suka zo tashar Unguwar Sarki suka tarwatsa su suka hana lodin daga bisani Kuma suka Saka motar janye Mota ta kwashe wasu daga ciki Motocin Gombe Line zuwa tashar Mando.

Yanzu haka Gombe Line ta fusata tare da daukar matakin Koro Yan Kaduna Line dake cin Karen su babu babbaka a Tashar su dake Jihar Gombe su ma.

Tashar Unguwar Sarki ta Gombe Line, ta kwashe sama da Shekaru 20 tana aikin ta tare da bin dukkan tsare-tsaren Gwamnatin Jihar Kaduna.

Daga Shuaibu Abdullahi 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org