Saka zai shafe sama da mako 2 ya na jinya - Arsenal
Kocin Arsenal, Mikel Arteta ya ce ɗan wasan gaban ƙungiyar Bukayo Saka zai yi jinyar fiye da wata biyu bayan an yi masa aiki a cinyarsa.
An yi canjin ɗan wasan gefen mai shekara 23 a kafin a tafi gurin rabin lokaci a wasan da ƙungiyarsa ta doke Crystal Palace da ci 5-1 a gasar Premier League ranar 21 ga watan Disamba.
Saka ya kasance ɗan wasa mai matuƙar muhimmanci ga ƙungiyar Arsenal, inda a kakar wasa ta bana ya zura ƙwallo tara sannan ya taimaka aka ci 13 a wasa 24 da ya buga a bana.
A baya kocin ƙungiyar ya ce ɗan wasan zai yi jinyar makonni, to amma a yanzu ce jinyar ka iya kai Saka fiye da wta biyu.
"Na yi ta cewa makonni masu yawa a baya, amma a yanzu ina tunanin zai kai fiye da wata biyu. Ban ma san haƙiƙanin lokacin da zai warke ba''.
BBC Hausa