Shahararrun ƴan Kannywood da suka yi mutuwar far daya (fuju'a).

Mafi yawancin mutane sun yi sun yarda da cewa  komai daren daɗewa wata rana su, da duk wani mai rai za su mutu amma akan shiga hali na kaɗuwa da ɗimauta idan wani na kusa ya mutu ba tare da tsammani ko kuma wata alama ba.

Wannan ya sa har yanzu masana'antar Kannywood da masu bibiyarta ba su fita daga jimamin rasuwar fitaccen mawaƙi, Elmu'az Birniwa ba.

Marigayin ya rasu ne a daren Laraba, 4 ga watan Disamban, kuma ya rasu ya bar mata biyu da yara shida.

Wani abu da ya ja hankalin mutane shi ne irin yadda ya yi rasuwar fuju'a, kasancewar lafiya ƙalau ya je filin wasan ƙwallon ƙafa na shirye-shiryen bikin abokin aikinsa mawaƙi Auta Waziri, amma sai dai aka samu labarin rasuwarsa.

Ba wannan ba ne karo na farko da ake samun irin mutuwar a Kannywood, inda a baya an samu wasu fitattun ƴan masana'antar da suka yi rasuwar ta farat-ɗaya, lamarin da ke girgiza masana'antar tare da jefa ta cikin jimami na tsawon lokaci.

Wannan ya sa BBC ta rairayo wasu daga cikin waɗanda suka yi rasuwar fuju'a a masana'antar a baya-bayan nan.

Aminu S. Bono

Aminu S. Bono fitaccen darakta ne a masana'antar Kannywood wanda ya rasu a ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamban shekarar 2023.

Marigayin ya yi rasuwar farat-ɗaya ne bayan ya dawo daga aiki, inda ya yanke jiki ya faɗi a cikin gidansa, sannan jim kaɗan aka samu labarin rasuwarsa.

An yi jana'izarsa ranar Talata da misalin ƙarfe 8:00 na safe a unguwar Ɗandago da ke cikin ƙwaryar birnin Kano.

Nura Mustapha Waye


A safiyar Lahadi, 3 ga watan Yulin 2022 ne aka wayi gari da rasuwar daraktan fim ɗin Izzar So, Nura Mustapha Waye.

Shi ma Mustapha an yi ban-kwana da shi lafiya ƙalau a daren Asabar, amma aka wayi gari ranar Lahadi ya rasu.


Saratu Daso

A daren ranar Talata 9 ga Afrilun 2024, wadda ta zo daidai da jajibirin sallah ne Allah ya yi wa Saratu Gidado , wadda aka fi sani da Daso rasuwa.

An ruwaito cewa lafiya ƙalau ta rabu da iyalanta a daren, kowa ya je ya kwanta, sannan har ma ma ta yi sahur ɗin azumi, amma da gari ya waye, sai dai aka ɗauko gawarta a ɗakinta.


El-Muaz Birniwa

Fitaccen mawaƙi, El-mu'az ya rasu ne bayan ya je wasan ƙwallon ƙafa na bikin mawaƙi Auta Waziri.

Rahotanni sun nuna cewa da ji wani iri a jikinsa sai ya fita, amma yana fita sai ya faɗi, kafin a ƙarasa asibiti ya ce ga garinku.

Binta Ola Katsina

A ranar Alhamis, 4 ga Oktoban 2023 ne jaruma Binta Ola Katsina ta rasu.

Ita ma ta rasu ne bayan ta kammala shirye-shiryen bikin Mauludi a ranar Laraba, amma aka wayi gari ta rasu.

Wannan na ɗaya daga cikin manyan silar mutuwar fuju'a.

Wasu daga cikin abubuwan da suke haifar da wannan matsala sun haɗa da shan taba, da ciwon sukari, da hawan jini, da ƙibar da ta wuce kima, da rashin motsa jiki, da kaɗuwa da shan miyagun ƙwayoyi.

Bugun jini

'Cerebrovascular accident' wanda akan kira shi da 'Stroke' shi ne lokacin da jini ya kasa isa zuwa cikin wani ɓangare na ƙwaƙwalwa ko dai sanadiyyar toshewar jijiya ko kuma fashewar jijiyar. Wannan yanayi kan sanya wasu daga cikin ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa su mutu.

Rashin samun kulawa cikin gaggawa zai iya haifar da lalacewar ƙwaƙwalwa baki ɗayanta.

Wasu daga cikin alamun bugun jini sun haɗa da jiri, da rashin iya magana da kyau, da rashin fahimtar abin da wasu ke faɗa, da rashin gani da kyau da ciwon kai nan take.

Toshewar huhu

Wannan kan samo asali ne daga toshewar jijiya a wani ɓangare na jikin ɗan'Adam, musamman ƙafa, inda gundulmin kan tafi zuwa cikin huhu ya toshe hanyar ficewar jini ta cikin huhu.

Wannan kan haifar da mutuwar ɓangaren huhu da lamarin ya shafa, wanda hakan zai hana huhu ya samar da iska ga sauran sassan jiki.

Hakan na iya yin barazana ga rayuwa matuƙar ba a ɗauki mataki cikin hanzari ba.

Lamarin zai iya tsayar da bugun zuciya ko kuma rikirkita harbawar jini daga cikin zuciya.

Kashi ɗaya cikin uku na waɗanda ke samun kansu cikin wannan yanayi na mutuwa.

Yadda za a ceci mutum

Duk mutumin da ya gamu da ɗaya da cikin matsalolin da ke janyo mutuwar fuju'a kamar yadda likita ya yi bayani a baya, to ba abin da yake buƙata da ya wuce a garzaya da shi asibiti.

Sai dai kafin kaiwa ga asibiti ko samun likita da zai kula da shi, maras lafiyar na buƙatar kulawar gaggawa ta farfaɗo da aikin zuciyarsa wadda a sau da dama take tsayawa da aiki a yayin da mutum ya samu kansa a wannan yanayi.

A wata zantawa da BBC ta yi da Farfesa Kamilu Musa Ƙaraye, wanda likitan zuciya ne a asibitin koyarwa na Mallam Amnu Kano a baya, ya yi bayani kan abin da ya kamata waɗanda ke tare da maras lafiyar ya su yi domin ganin nunfashin mutum ko zuciyarsa ba ta tsaya da aiki ba.

Likitan ya bayyana abin da ake kira a Turance kuma a takaice ''CPR'' (Cardiopulmonary resuscitation), inda wani da ya ke da ƙwarewa da wannan hanya zai riƙa danna ƙirjin maras lafiyar, a-kai-a-kai, domin taimaka wa zuciyar ta ci gaba da aiki har zuwa lokacin da za a kai ga asibiti.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org