Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin Ya Bayyana Dangantakar Rasha da Kasar Sin a Matsayin Mafi Karfi da Aka Taba Samu a tarihi.
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya bayyana cewa dangantakar tsakanin Rasha da kasar Sin ta kai wani mataki na musamman wanda bai taba kasancewa ba a baya, sakamakon babban amincewa da ke tsakanin kasashen biyu.
Putin ya jaddada cewa kasashen suna da cikakken hadin kai a matakin kasa da kasa, inda suke goyon bayan juna kan batutuwa kamar yaki da shisshigin waje, kare ikon mulkin kai da cikakken yankin kasashen su, da kuma tabbatar da adalci a tsarin duniya.
ATP Hausa