Sojoji sun lalata maboyar ƴan bindiga tare ƙwato makamai da oota a Taraba da Benue
Sojojin Runduna ta 6 na Rundunar Sojan Nijeriya/Sashe na 3 na Operation Whirl Stroke (OPWS) sun samu gagarumar nasara a ci gaba da aikin soji na dawo da zaman lafiya da tsaro a Jihar Taraba da wasu sassan Jihar Benue karkashin shirin "Operation Golden Peace."
A ranar 7 ga Disamba, 2024, sojojin sun gudanar da aikin kawar da bata gari da aka tsara sosai a yankunan Akahagu da China a Karamar Hukumar Ukum, Jihar Benue.
An ci gaba da aikin zuwa kauyen Ikayor, inda sojojin suka fafata da ‘yan bindiga a wani sansani da aka danganta da sanannen dan ta’adda da ake nema ruwa a jallo, Akiki Utiv, wanda aka fi sani da “Full Fire.”
A lokacin arangamar, sojojin sun yi amfani da karfin wuta mai yawa, wanda ya tilasta wa ‘yan bindigar tserewa cikin rudani da barin sansaninsu.
Bayan fafatawar, an kwato wata mota kirar Toyota Corolla ja da babur. A yayin binciken motar da aka bari, an gano wando na kamuflajin soji, bindigar Beretta tare da harsashi daya na 9mm, da wasu kayan daban.
Da yake magana kan aikin, Kwamandan Runduna ta 6, Birgediya Janar Kingsley Uwa, ya jinjinawa sojojin bisa jarumtaka da jajircewarsu duk da kalubalen da suke fuskanta. Ya kuma tabbatar wa mazauna Taraba da Benue karkashin Sashe na 3 na OPWS cewa sojoji za su ci gaba da kasancewa masu jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai masu inganci da na lokaci don taimakawa kokarin hukumomin tsaro.