Sojoji Sun Yi Ram da Mata da Ke Samar da Makamai ga Bello Turji, an Cafke Dan Acaba
An same ta da alburusai da bindigogi a kokarin kai wa yan fashi.
Sojoji Sun Yi Ram da Mata da Ke Samar da Makamai ga Bello Turji, an Cafke Dan Acaba
Rundunar sojojin 'Operation Fansar Yamma' ta kama wata mata mai shekaru 25 da ake zargin tana safarar bindigogi da alburusai 764 zuwa ga ƴan fashi Kakakin sojoji ya bayyana cewa an kama matar da wani abokin tafiyarta ne a Badarawa, karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara Rahoton sirri ya kai ga cafke su yayin da suke kan hanyarsu daga Kware zuwa Badarawa da makaman da ake zargin za su kai ga Bello Turji
Jihar Zamfara - Rundunar sojoji ta yi nasarar cafke wata mata ɗauke da alburusai 764 da bindigogi 6 da ake zargin za ta kai ga Bello Turji. Rundunar sojojin ta 'Operation Fansar Yamma ta samu' ta cafke matar mai shekaru 25 da abokin harkarta a karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara.
Sojoji sun cafke masu ba Turji makamai Kakakin rundunar, Laftanar-kanal Abubakar Abdullahi, ya ce an kama matar ne tare da abokin tafiyarta ranar 28 Disamba 2024 a Badarawa, cewar Zagazola Makama.