Tare da sanin Mahukuntan Najeriya ake shirya wa kasarmu makarkashiya._ Shugaban Nijar janar Tchani
A cikin wata tattaunawar da shugaban kasar ya yi da gidan talabijin na kasa a yau laraba ya ce Faransa ta kafa wani sansanin yan ta'adda a dajin Gaba dake cikin jahar sokoto da niyyar hargitsa kasar Nijar.
Shugaban kasar ya ce yan ta'addan da suka kama ne suka sanar da su hakan.
Domin guduwa tare Mahukuntan Na Nijar sun sanar da takwarorin su na tarayyar Najeriya abin da ke faru, har ma wani mai suna Ahmad Abubakar Rufa'i ya zo Nijar ya kuma gana da yan ta'addan . Amma daga baya sun gane cewa Rufa'in na daya daga cikin wadanda yan ta'addan ke hada kai da su.
Wanda yake son ya saurari bayanan Tchiani akwai bidiyo a Telegram channel ta nan
👇
https://youtu.be/u6EZclFs68k?si=N-tcSr9mTnVlNUd7
Muryar Nijar TV