Tinubu ya jinjinawa Ganduje bisa samun nasara ta ban mamaki a yayin zabuka
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya Dr. Abdullahi Umar Ganduje, CON, Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, murnar cika shekara 75 a ranar 25 ga Disamba, 2024.
Shugaba Tinubu ya yaba wa Dr. Ganduje, abokin siyasar sa kuma na kusa, bisa jagoranci na musamman, jajircewarsa, da kuma gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.
Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan fannin yada labarai Bayo Onanuga ya fitar a ranar Laraba.
Shugaban ya jinjina wa Dr. Ganduje bisa jagorancin sa na koyi a matsayin Shugaban Jam’iyya, wanda ya jagoranci samun nasarori masu ban mamaki a zabuka. Ya kuma lura cewa kokarin Dr. Ganduje da tawagarsa na kara karfafa jam’iyyar da hada kan mambobinta don cimma burin ci gaban kasa.
Shugaba Tinubu ya nuna godiya ga shawarar manufofi, goyon baya mara yankewa, da jajircewar Dr. Ganduje. Ya kuma karfafa masa gwiwa da ya ci gaba da aiki tukuru tare da irin wannan karsashi da kishin da ya saba nuna wa. Shugaban ya bayyana Dr. Ganduje a matsayin wanda ya jajirce wajen kare dimokuradiyya bisa doka da kuma bayar da gudunmawa ta tsawon shekaru a hidimar jama’a.
"Shugaba Tinubu ya tuno da gudunmawar Dr. Ganduje ga hidimar jama’a tun daga farkon rawar da ya taka a matsayin daya daga cikin ma’aikatan gwamnatin farko da suka kula da harkokin Babban Birnin Tarayya (FCT) da kuma matsayin sa a matsayin kwamishina a Jihar Kano a shekarun 1990."
Daily Nigeria Hausa