Tinubu zai yi amfani da na'urar AI ya yaƙi rashin tsaro a Nijeriya - Sanata Jimoh
Sanata mai wakiltar Ondo ta kudu, Jimoh Ibrahim, ya ce shugaban kasa Bola Tinubu zai yi amfani da na'urar fasaha ta zamani ta AI wajen yaki da kalubalen tsaro a kasar.
Ibrahim yayi wannan batu ne a jiya Laraba lokacin da ya baiyana a shirin Siyasa a Yau, wani shiri na gidan Talabijin na Channels.
Sanatan ya ce shugaban kasar ya ware Naira tiriliyan 5 ne a fannin tsaro saboda yana son a rika amfani da fasahar zamani a yakin da ake yi da ‘yan bindiga da masu tayar da kayar baya.
"Shi Shugaba Tinubu, ko kuna so ko ba kwa so, ni ba mai magana da yawunsa ba ne, amma dai an fara ganin cewa tsaro yana inganta”in ji shi