Trump Ya nemi Kasar Canada ta zama jiha a cikin Amurka.
Tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ja hankalin jama’a bayan ya wallafa hoton tutar kasar Kanada tare da wani karin bayani da ya nuna cewa Kanada na iya shiga Amurka a matsayin jiha ta 51. Wannan batu ya taso ne bayan wata hira da ya yi, inda ya yi tayin cewa Amurka za ta iya daukar Kanada don kara karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Trump ya yi wannan maganar ne cikin salo na barkwanci, amma ya ja hankalin masu sharhi da dama a kafafen sada zumunta. Bugu da kari, abin ya haifar da martani daga ‘yan Kanada da kuma shugabannin kasar, ciki har da Firaminista Justin Trudeau, wadanda suka bayyana cewa Kanada kasa ce mai ‘yanci kuma tana alfahari da cikakken ikon kanta.
Wannan furuci ya kara nuna salon mulkin Trump da yadda yake jan hankali ta kafafen sada zumunta, musamman a lokacin da ake kara karkata hankula kan batun zaben shugaban kasa a shekarar 2024.
@ATP Hausa