Tsoffin sojoji sun rufe ma’aikatar kudi a Abuja
Wasu daga cikin tsofaffin sojojin Najeriya karkashin kungiyar Coalition of Military Pensioners sun rufe Ma’aikatar Kudi ta Tarayya a Abuja da safiyar Alhamis saboda rashin biyan karin albashi daga kashi 20% zuwa 28% daga watan Janairu zuwa Nuwamba 2024.
Tsofaffin jami’an sojojin da suka zo daga sassa daban-daban sun nuna takaicinsu game da gazawar Gwamnatin Tarayya wajen biyansu hakkokinsu.
Bukatun su sun hada da:
Biyan tallafin rayuwa daga Oktoba 2023 zuwa Nuwamba 2024.
Biyan karin N32,000 ga fanshon su.
Biyan kudin Security Debarment Allowance (SDA) gaba daya.
Dawowar kudaden da aka cire daga fanshon sojojin da aka sauke saboda rashin lafiya, da sauransu.