Tsohon sanata, Shehu Sani, martani kan kalaman malam Nasiru El-Rufai da yayi akan Tinubu.

 Shwhu sani ya yi Allah wadai da nasihar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi kan batun cin hanci da rashawa da ake zargi a kamfanin mai na Najeriya (NNPCL).

Sani, wanda ya wakilci Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawan ta 8th. ya caccaki El-Rufai a ranar Lahadi, yana mai  bayyana cewa "bai kamata a dauki maganar Malam Nasiru El-Rufai da muhimmanci ba, domin bai yi suka ba a lokacin mulkin Muhammadu Buhari na tsawon shekaru 8 da suka gabata. 

Sani ya ce, "Akwai mutane da suka yi shuru lokacin da Buhari ke nadin mukaman siyasa irin na dangi, amma yanzu sun samu damar yin magana lokacin da lamarin bai dace da su ba."

Tsohon sanatan ya kara da cewa, " A lokacin mulkin El-Rufai ne Kudancin Kaduna  ta zama yankin wariya tsawon shekaru takwas 

A cewar Shehu Sani, duk wanda zai iya magana ko yin suka ga Shugaba Tinubu kan batutuwan da suka shafi nadin mukaman gwamnati da ake zargin suna nuna bambanci ko cin hanci, bai kamata a ce maganar ta fito daga bakin  El-Rufai ba.

A cewar wannan masanin, Tinubu ya zabi yin rinjaye a tattalin arziki da mutane daga kudu maso yamma, kamar yadda tsohon Shugaba Buhari ya shahara da nadin manyan mukaman tsaro da ‘yan arewa a lokacin mulkinsa.

@A T P Hausa 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org