Tsohon shugaban NLC na jihar Edo ya faɗi matacce yayin taƙaddama da ƴansanda
Kwamishinan ƴansanda a jihar Edo, Umoru P. Ozigi ya bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin da ya haifar da mutuwar Kaduna Eboigbodin, tsohon shugaban ƙungiyar ƴan ƙwadago a shine binciken ƴansanda a birnin Benin.
Wasu majiyoyi sun baiyana cewa Eboigbodan ya mutu ne yayin taƙaddama da ƴansanda, waɗanda su ka nemi ya nuna musu takardun motarsa a wani shine bincike.
Majiyoyin sun ce lokacin da Eboigbodan, wanda ke tare da matar sa a motar, ya nuna musu takardun motar sai ya mika musu.
Daga nan ne sai taƙaddama ta ɓarke tsakanin su bayan da ƴansandan su ka zargi tsohon shugaban NLC din da cewa motar ta sa ta sata ce.
Majiyoyin sun ce bayan ya fito a fusace yana ta hayaniya, sai kawai aka ga ya yanke jiki ya faɗi.
Majiyoyin sun yi zargin cewa faduwar da ya yi sai ƴansandan su ka gudu daga wajen, inda su ka bar matar sa, wacce ta garzaya da shi asibiti kuma a nan aka ce mata ya mutu.
@Daily Nigeria Hausa