Turmutsutsu: Sufeto Janar na ƴasanda Ya Haramta Rarraba Tallafin Abinci da tarukan nishadi ba bisa ka’ida ba
Sufeto Janar na ‘Yasanda , Kayode Egbetokun, ya gargadi al’ummar kasa a ranar Asabar kan rarraba tallafin abinci da tarukan nishadi ba bisa ka’ida ba a fadin kasa.
Egbetokun ya nuna damuwa kan yadda ake gudanar da rarraba tallafin abinci da kayan agaji cikin rashin tsari, musamman a wannan lokaci na bukukuwa.
Ya ce wannan al’amari yana da matukar tayar da hankali kuma yana bukatar daukar matakin gaggawa don kare rayukan al’umma, musamman matasa masu rauni da tsofaffi.
Gargadin ya biyo bayan wasu munanan hadurran da suka faru kwanan nan, wadanda suka nuna bukatar samar da tsari mai kyau da ingantaccen hanyar isar da kayan tallafi ga al’umma masu bukata da jama’a baki daya.
Idan za a iya tunawa cewa a ranar 18 ga watan Disamba, 2024, wani mummunan al’amari ya faru a Ibadan, Jihar Oyo, inda turmutsitsin da ya faru a wani taron nishadi na yara ya yi sanadin mutuwar yara 35, tare da jikkata wasu da dama.
Da safiyar yau, 21 ga watan Disamba, 2024, wani mummunan al’amari ya sake faruwa a Cocin Katolika na Holy Trinity, Maitama, yayin wani turmutsitsi da ya faru a lokacin rarraba kayan abinci ga tsofaffi da masu bukata ta musamman.