Wani Dan sanda Ya Ce 'Mutane sun sun fi 100 suka kawo mana hari'

 Wani dan sanda ya bayyana yadda aka kai musu farmaki a Ondo.

Ana zargin 'yan acaba ne suka kai farmakin kuma sun raunata babban jami'i. 

Tarin 'Yan Acaba Sun Kai Hari Caji Ofis, Sun yi wa 'Yan Sanda Rubdugu 

Ana zargin 'yan acaba sun kai hari kan ofishin 'yan sanda a Oka-Akoko a jihar Ondo sakamakon rashin jituwa da aka samu Wata majiya ta bayyana cewa 'yan acaban sun zargi 'yan sandan da boye direban mota da ya lalata babur din ɗaya daga cikin abokan aikinsu Rahotanni sun nuna cewa 'yan acaban sun ji wa jami'an 'yan sanda rauni tare da kwace wayar hannu ta wani babban jami'in 'yan sanda 

Jihar ondo - Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu 'yan acaba sun kai hari kan ofishin 'yan sanda a Oka-Akoko, karamar hukumar Akoko ta Kudu maso Yamma a Jihar Ondo. An kai harin ne bayan wata hatsaniya da suka ce direban mota ya haddasa, inda ya lalata babur din ɗaya daga cikinsu. 

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa harin ya yi sanadin raunin wasu jami'an 'yan sanda, inda aka kuma kwace wata wayar hannu ta wani babban jami'in ofishin.


@Legit ng Hausa

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org