Wani Matashi Mai Jini A jika Ya Mutu a Hannun Yan Sanda.
Basarake a Arewa Ya Bukaci Kaddamar da Bincike Kan Mutuwars
Wani Matashi Ya Mutu a Hannun Yan Sanda, Basarake a Arewa Ya Bukaci Kaddamar da Bincike 0 Lahadi, Disamba 22, 2024 at 11:15 Yamma daga Abdullahi Abubakar 2 - tsawon mintuna Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya bukaci yan sanda su binciki mutuwar Jimoh AbdulQodir a hannun jami'ansu Iyalan marigayin sun yi zargin cin zarafi da neman boye gaskiya, suna rokon hukumomi su dauki mataki Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kwara ta tabbatar da mutuwar AbdulQodir, tana mai cewa za a gudanar da cikakken bincike
Jihar Kwara - Sarkin Ilorin a jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya bukaci bincike kan mutuwar matashi a hannun yan sanda. Basaraken ya bukaci Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya kafa kwamitin bincike kan mutuwar Jimoh AbdulQodir.
Wani matashi ya rasa ransa a hannun yan sanda, sarkin Ilorin ya bukaci kaddamar da bincike. Hoto: Legit. Asali: Original
AbdulQodir: Basarake ya bukaci kaddamar da bincike LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng Punch ta ce marigayin ya mutu ne a hannun ‘yan sanda a Ilorin a Kwara a ranar Juma’a 20 ga watan Disambar 2024.
@Legit Hausa