Wike ya Ƙwace Filin Buhari, Tajudeen Abbas, George Akume, Uba Sani da wasu mutum 762
Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT), Nyesom Wike, ya soke izinin mallakar fili 762 a gundumar Maitama 1 da ke Abuja, saboda rashin biyan kudaden haraji
Cikin wadanda abun ya shafa akwai tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon cif Joji na Najeriya Chief Justice Walter Onnoghen, Gwamnan Kaduna, Uba Sani, Sakataren Gwamnatin tarayya SGF, George Akume, da kuma tsohon Gwamnan Imo, Rochas Okorocha da Ben Ayade.
Sauran wadanda Ministan ya kwace filayensu sun hada da Shugaban mai tsawatarwa na majalisa Sanata Tahir Monguno da Kakakin Majalisar Dattawa Abbas Tajudeen.