Yadda Malamin Jami'a da ya yi Garkuwa da Matar Shugaban ASUU ya Faɗa Komar Ƴan Sanda

 Rundunar ƴansandan jihar Benue ta cafke Dr Tersagh Ichor, malami a jami’ar Joseph Saawuan Tarka, JOSTUM, da ke Makurdi bisa zarginsa da shirya garkuwa da Susan Anyagh.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan, SP Sewuese Anene ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta rabawa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa a yau Juma’a a Makurdi.

A cewar PPRO din, an yi garkuwa da Mrs Anyagh, wacce ita ce uwargidan shugaban kungiyar malaman jami'o'i, ASUU, JOSTUM, a ranar 7 ga watan Disamba a Makurdi.

Anene ta ce an yi garkuwa da ita ne a kan titin Otukpo, a Makurdi kuma a cikin motarta zuwa inda ba a san inda take ba.

Ta ci gaba da cewa, kwamishinan ‘yan sandan jihar Binuwai, Steve Yabanet, nan take ya umarci dukkan jami’an da ke sintiri da shingayen binciken ababen hawa da su tabbatar da ceto ta tare da kamo wadanda ke da hannu a lamarin.

PPRO din ta bayyana cewa da misalin karfe 2 na rana a wannan rana, an kuma samu wani labarin a kan titin Yandev-Ugbema cewa wadanda suka sace ta sun kai mata hari kuma suka bar ta kwance a gefen hanya.

Anyagh ya shaida wa ‘yan sanda cewa, a lokacin da take tuki daga babban tashar NNPC da ke Kanshio, inda ta je karbar kudi daga hannun abokin cinikinta, wasu da suka yi ikirarin suna da bukata sun yi mata tuta a kan titin Otukpo, sai ta tsaya don ba da taimako.

A cikin sanarwar, Anene ta ce an kama Ichor ne a kan lamarin, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.

PPRO ta ce za a sanar da cikakkun bayanai game da binciken nan gaba.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org