Yadda Wani Mahaifi Ya Yi Wa 'Yarsa Ciki Sau Biyu – Uwargidan Gwamnan Bauchi ta bayyana wani labari mai cike da tausayi
Uwargidan Gwamnan Jihar Bauchi, Dr. Aishatu Bala Mohammed, ta bayyana wani labari mai cike da ban tausayi game da cin zarafi da fyade, inda wani mahaifi ya yi wa 'yarsa ciki har sau biyu.
Da take magana da manema labarai kan yaki da fyade da cin zarafin jinsi a jihar, Dr. Aishatu Bala Mohammed ta bayyana cewa
“Bayan mahaifiyarta ta rabu da mahaifinta, ita ce ta ci gaba da kula da 'yar. Sai dai daga baya, yarinyar ta roki mahaifiyarta da ta kai ta wurin mahaifinta saboda cin fuska da takura da abokananta ke yi mata suna cewa ba ta da uba. Mahaifiyar ta amince, amma mahaifin ya nemi ya sake aure da mahaifiyar. Bayan ta amince, ta bar yarinyar tare da mahaifin sannan ta tafi.
“Kafin ta dawo, mahaifin ya riga ya fara cin zarafin yarinyar. Yarinyar ta kai kuka ga mahaifiyarta, wadda ta fuskanci mahaifin. Mahaifin ya amsa laifinsa. Mahaifiyar ta dauki yarinyar zuwa asibiti, inda aka tabbatar cewa yarinyar tana dauke da cikin mahaifin.
“Abin bakin ciki, mahaifiyar ta mutu daga bugun zuciya jim kadan bayan haihuwar Yarinyar. Bayan rasuwarta, dangin mahaifiyar ta sun ki karbar yarinyar amma sun karbi jaririyar da aka haifa. Saboda haka, babu inda yarinyar ta iya komawa sai wurin mahaifin nata.”
Dr. Aishatu ta kara da cewa mahaifin bai daina cin zarafin yarinyar ba, duk da cewa ya kara aure. Lokacin da yarinyar ta shaida wa matar mahaifin game da abin da yake aikatawa, matar ta fuskance shi. Mahaifin ya amsa laifinsa, kuma matar ta bar shi. Duk da haka, mahaifin ya cigaba da cin zarafin yarinyar, Wanda ta sake kai ga daukar ciki karo na biyu. Bayan haihuwar jaririnta na biyu, makwabta sun kai rahoton lamarin ga hukumar Hisbah. Hisbah ta kama mahaifin, kuma kotu ta yanke masa hukuncin zaman kaso na shekaru bakwai.
Karaduwa Post Hausa