Yan Fashi Da Makami Sun Tare Tawagar Kungiyar Kwallon Kafar El Kanemi Warriors Ta Maiduguri.
'Fashi Da makamin ya farune a kan hanyarsu ta zuwa wasa abinda ya yi sanadiyar jikkata wasu daga cikin 'yan wasan da kuma shugabannin su.
Jaridar Rana24 ta ruwaito sun ce an tare motar 'yan wasan ne a kauyen Rijiyar Malam dake kan hanyar Bauchi zuwa Jos da misalin karfe 12 da minti 45 na dare jiya asabar.
Wani jami'in kungiyar Suleiman Abdullahi ya ce 'yan fashin dauke da adduna da wukake da kuma bindigogi sun tilasta musu fita daga cikin mota tare da karbe wayoyinsu da kuma wasu kadarori da suke dauke da shi.
Yayin da suka raunata akalla 'yan wasa 10. Kakakin rundunar 'Yan sandan jihar Bauchi Ahmed Wakil ya tabbatar da aukuwar lamarin.
📷 El Kanemi Warriors