Yan ta'addata sun kashe hakimi sun kona gidaje a cikin jihar Gombe

 An samu wasu Yan ta'addata ɗauke da muggan makamai sun kashe hakimi tare da ƙona gidaje da sace dabbobi da ba a san adadinsu ba a Ƙaramar Hukumar Ɓilliri da ke Jihar Gombe

Wasu mahara ɗauke da muggan makamai sun kashe hakimi tare da ƙona gidaje da amfanin gona sannan suka sace dabbobi da ba a san adaddinsu a yankin ƙaramar hukumar Tafawa Ɓilliri da ke Jihar Gombe.

Maharan da ake zargin makiyaya ne sun kutsa garin Powishi da ke yankin Kalmai ne a cikin dare inda suka kashe Hakimin, Malam Yusuf Akwara, sannan suka ci gaba da aika-aikan.

Da yake tabbatar da harin, kakakin ’yan sandan jihar Gombe ASP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa maharan sun shiga ƙauyen ne a kan babura a daren Laraba, inda suka tayar da tarzoma.

A safiyar Alhamis, DPO na Ƙaramar Hukumar Ɓilliri ya sanar da rundunar game da harin, inda ta tura tawagar hadin gwiwa ta ’yan sanda da sojoji zuwa wajen domin shawo kan lamarin.


Trust Radio

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org