YANZU-YANZU: Mutane 10 Sun Rasa Ransu a Turmutsitsin Karɓan Abinci a Wani Cocin a Abuja
Aƙalla mutane 10 ne aka ruwaito sun mutu, a yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon turmutsitsin da aka yi a cocin Holy Trinity Catholic Church da ke Maitama a birnin Tarayya Abuja da safiyar yau Asabar.
Idan dai ba a manta ba a kwanakin baya kaɗan ne aka samu irin wannan lamari a garin Ibadan na jihar Oyo, inda wani turmutsitsin da ya auku a wajen bikin baje kolin yara ya yi sanadiyar mutuwar yara aƙalla 35 tare da jikkata wasu shida.
Jaridar Punch ta labarto cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar a lokacin da mazauna yankin suka hallara domin karɓar kayan agajin da cocin za ta raba.
@Sahara Reportes