Zamu kayar da Duk Wani ɗan Arewa wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 Har Sai Bola Tinubu ya gama yin Shekaru 8 Tukunnka, inji Shugaban jam'iyyar Apc Ganduje

 DAGA Wakiliya  Ganduje ya shawarci manyan ‘yan siyasa daga Arewa da ke shirin tsayawa takarar shugabancin kasa a 2027 da su jinkirta wannan buri har zuwa 2031, lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kammala wa’adinsa na biyu.  

Da yake magana a wani shirin siyasa na TVC a ranar Alhamis, Ganduje ya yi kira ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, da ya hakura da tunanin komawa fadar Shugaban Kasa a 2027, yana mai cewa idan Allah ya kaddara zai zama shugaban kasa, zai iya nasara har a shekara 90.  


Ya kara da cewa, har yanzu lokacin kudu ne don samar da shugaban kasa a 2027. Akume ya bayyana cewa manufofin tattalin arziki da tsarin haraji da Shugaba Tinubu ya dauka cikin watanni 17 na mulkinsa sun dace, kuma yana da kyakkyawar fatan cewa zai yi wa’adi biyu na mulki.  


Ya bayyana cewa, "Shugaba Tinubu, a matsayin sa na dan kudu, ya kamata a bashi damar kammala wa’adi na biyu. Don haka, wadanda ke da niyyar tsayawa takara daga Arewa a 2027 su kalli bayan wannan shekarar, su jira har zuwa 2031."  


Har ila yau, Akume ya bukaci ‘yan Najeriya da su ba wa kudurorin haraji damar wucewa matakan majalisar dokoki, yana mai cewa suna da kyau don inganta kasar.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org