Zanga-zanga ta ɓarke a Koriya ta Kudu bayan ayyana dokar ta- baci.
Shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol ya ayyana dokar ta-baci, yana zargin 'yan adawa da kasancewa "makiyan kasar,".
Daruruwan masu zanga-zanga sun taru a harabar majalisar dokoki suna neman a bar su su shiga, yayin da 'yan sanda ke cigaba da bada tsaro.