A cikin watanni takwas na farko na mulkinsa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje har sau 14,.
Duk da cewa tafiye-tafiyen sun kasance da nufin haɓaka dangantakar diplomasiyya da jawo hannun jari, an yi hasashen cewa an kashe sama da Naira biliyan 2.3 wajen waɗannan tafiye-tafiyen daga watan Fabrairu zuwa Yuli 2024.
A wa'adin mulkinsa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci ƙasar Faransa sau biyu. Ziyarar farko ta kasance a watan Yuni 2023, inda ya halarci taron sabuwar yarjejeniya ta kuɗi ta duniya a birnin Paris. Bayan kammala wannan taro, ya tashi daga Faransa zuwa Landan domin wata gajeriyar ziyara. Ziyarar ta biyu kuwa ta faru ne a ranar 11 ga watan Oktoba, 2024, lokacin da ya wuce daga Landan zuwa Paris domin gudanar da wasu ayyuka masu muhimmanci.
A cewar rahoton da aka wallafa a ranar 2 ga Janairu, 2025, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shafe kwanaki 180 daga cikin kwanaki 584 na mulkinsa a ƙasashen waje.
Duk da cewa wannan rahoto bai fayyace yawan tafiye-tafiyen da ya yi a shekarar 2025 ba, kasafin kuɗi na shekarar 2025 ya nuna an ware Naira biliyan 6.14 domin tafiye-tafiyen shugaban ƙasa zuwa ƙasashen waje.
Wannan ya nuna cewa ana sa ran Shugaba Tinubu zai ci gaba da yin tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje a shekarar 2025.