A WATAN RAJAB: A KA YI AUREN MAHAIFAN ANNABI (SAWW) ABDULLAHI DA AMINA (AS)

 Na'am, an auren mahaifan Annabi Muhammad (AS) ne a cikin watan Rajab: sai dai malaman tarihi basu tattance ranar ba.

Abdulmuttalib (AS) ya zaɓi Amina bint Wahb (AS) daga kabilar zuhur ta zama matar dansa Abdullahi. A lokacin Amina ta kasance mafi kyawun macen Kuraishawa a tsatso da matsayi.


Wata ‘yar duba daga Tibala wacce aka fi sani da Fatimah bint Murr al-Khath’amiyah ita ma ta ga Abdullahi. Wannan mata ta kasance daya daga cikin mafi kyawu da tsaftar matan larabawa. Sai ta ga hasken annabci a fuskar Abdullahi, sai ta mika masa bukatar aurenta amma ya ki yarda da ita.


Labarin wani Annabi da zai zo daga ‘ya’yan Isma’il (amincin Allah ya tabbata a gare shi) yana yaduwa a tsakanin Larabawa a ko’ina a cikin yankin. Wannan labari ya dogara ne akan abin da ma'abuta littafi suka ba da labari da abin da suke ba da labari daga abin da aka rubuta a cikin Attaura, a fakaice da bayyane. Har ila yau, mutane sun gano hakan daga masu duba da masu ilmin taurari.


Duk da Abdullahi bn Abdul Muddalib (AS) matashi ne kyakkyawa, ya mallaki tarbiyya mai ban mamaki da daukaka saboda cewa yana da tsafta da kyawawan dabi'u yan mata da yawa sun nemi aurensa, amma Allah ya kaddara cewa Amina za ta kasance Matar Abdullah.


Amina ta haihu Annabi mai daraja. Bayan 'yan watanni da daukar ciki, Abdullahi ya yi tafiya zuwa kasar Sham (Syriya bisa ga ma'anar yanayin kasa na Larabawa yanki ne da ya kunshi Palastinu, Jordan, Siriya da Lebanon da Birnin Gaza da ke gabar tekun Palastinu). daya daga cikin manyan garuruwan da ‘yan kasuwar Kuraishawa suke yawan zuwa). Amma a kan hanyarsa ta dawowa sai ya kamu da rashin lafiya, ya zauna a wurin kawunsa na uwayensa daga kabilar Bani Najjaar a Yasriba, inda suka rinka kula da shi. A inda ya rasu ne saboda rashin lafiyar da ya yi fama da ita.


Amina ta ji takaicin rasuwar mijin da take so, wanda ya zauna da ita watanni kadan bayan aurensu. Kuka takeyi tana kuka sosai dan ta riga ta zama maitakaba tun ba'a haihu ba. Amma ta hakura ta daure. Ta sami kulawa sosai daga Abdul-Muddalib. Wasu rahotannin tarihi sun nuna cewa, Abdullahi ya rasu jim kadan bayan haifuwar Manzon Allah (SAWW). 


Haihuwar Muhammad (SAWW).


Ta haife shi ne a ranar 12 ga watan Rabiu'auwal, 570. Labarin haihuwarsa ya ba Banu Hashim farin ciki sosai har Abu Lahab ya 'yanta kuyangarsa Thuwayba al-Aslamiyya wacce ta kawo labarin haihuwar. Abdul al-Muttalib ya sa masa suna Muhammad. Da Kuraishawa ta tambayi sunan jikansa, sai ya ce: “Ina son a yabe shi sama da kasa.

Tafiya zuwa Madina da Mutuwa

Amina ta dauki Muhammad don ta ziyarci kabarin mijinta Abdullah a madina a shekara ta bakwai ta giwaye. Kawun mahaifin Annabi Muhammad (SAWW) daga Banu Najjar ne. Ta yi rashin lafiya lokacin da ta dawo daga Madina ta rasu a al-Abwa'  Ummu Ayman ta dawo da Annabi Muhammad (SAWW) zuwa Makka bayan kwana biyar.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org