An ɗaure tsohuwar ma'aikaciyar gidan yari bisa laifin yin lalata da wani ɗaurarre
An ɗaure wata tsohuwar jami'ia a gidan yari na HMP Wandsworth na tsawon watanni 15, bayan an gan ta a faifen bidiyo ta na lalata da wani fursuna.
Manyan ma’aikatan gidan yarin ne suka gano Linda De Sousa Abreu bayan da aka yada faifan bidiyon ta yanar gizo.
Gwamnan na Wandsworth ya ce abin da Abreu ta yi na lokaci kankani, ya rusa duk aikin da aka yi na tsawon shekaru na na kare ma'aikata mata a gidajen yari na maza.
Abreu, mai shekaru 30, wacce aka kama a filin jirgin sama na Heathrow kafin ta yi yunkurin hawa jirgi zuwa Madrid tare da mahaifinta, a baya ta amsa laifin rashin da'a a ofishin gwamnati.
An ɗauki bidiyo ɗin Abreu da fursunan a cikin ɗaki tsakanin 26 da 28 ga Yuni.
Rundunar ƴansanda ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan fursunonin biyu da aka gano a cikin bidiyon.
An kuma shaida wa kotun cewa an sake samun wani faifan bidiyo na yadda ta yi lalata da wani fursuna a kyamarar aikin da gidan yari ya rabawa ma'aikata, wacce ake saka wa a jikin kaya, inda Abreu ta amsa laifin yin lalata da fursunan.