Ƴan bindiga sun kashe ƴan bijilanti 21 a jihar Katsina

 Aƙalla ƴan bijilanti da ke taimaka wa Gwamnnati wajen yaƙi da ƴan ta'adda su 21 ne suka mutu a wani harin kwanton bauna da ƴan fashin jeji su ka yi a Jihar Katsina.

Kakakin rundunar ƴan sandan Katsina, Abubakar Sadiq Aliyu, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP a yau Asabar cewa, wani ayarin mayakan da ke marawa gwamnati baya na dawowa daga gaisuwar ta'aziyya ga iyalan wani abokin aikinsu da ya mutu, sai aka kai musu hari a kauyen Baure da ke yankin Safana.


"Abin takaici, mutane 21 sun rasa rayukansu sakamakon harin,” in ji Aliyu, yana mai cewa ‘yansanda su na kan bincike don tabbatar da cafke wadanda su ka aikata harin da ya faru a ranar Talata.

Shaidu, duk da haka, sun shaida wa jaridar Premium Times ta Najeriya cewa  mutane 25 aka kashe a harin, yayin da wasu mazauna kauyen su ka ɓace.

An rawaito cewa mayakan da aka kai wa harin suna cikin kungiyar sa-kai ta Katsina Community Watch Corps (KCWC) da gwamnati ke tallafawa.

Jaridar ta kuma nakalto Aliyu yana cewa an tura ‘yansanda zuwa yankin da aka kai harin don dawo da zaman lafiya.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org