Ana samun ci gaba wajen tattaunawa a cinikin dan bayan Manchester City, Kyle Walker, tsakanin ƙungiyar da AC Milan.
Fabrizio Romano ya rawaito cewa Walker na don sauya sheƙa zuwa Milan kuma idan ta tabbata, zai rattaba hannu kan kwantaragi ta shekaru biyu, zuwa 2027 kenan.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Erling Haaland ya rattaba hannu kan tsawaita kwantaragin sa ta dogon lokaci da ƙungiyar, wanda zai ci gaba da zama a Etihad har zuwa 2034.
Dan kasar Norway din ya koma City ne daga Dortmund a 2022 kuma ya zura kwallaye 111 a wasanni 126 da ya buga wa City tun daga lokacin.
Yarjejeniyar da dan wasan ya kulla a baya, wadda rahotanni suka ce ta hada da sharadin sayar da shi, za ta ta kare ne a 2027.
Sabon kwantiragin Haaland zai sa dan wasan ya ci gaba da zama a City har zuwa ranar da ya cika shekaru 34 da haihuwa idan ya ci gaba da zama a kungiyar har zuwa karshen shekara tara da rabi nan gaba.