Ɗansanda mai muƙamin ACP, Daniel Amah ya musulunta
Wani shahararren ɗansanda mai muƙamin Mataimakin Kwamishinan Ƴansanda, ACP, Daniel Amah ya karɓi addinin Musulunci.
Amah, wanda yanzu sunan sa ya koma Muhammad Sanusi, ya daɗe ya na hidimtawa Musulunci a rayuwar sa.
A wani saƙo da fitaccen dan jaridar nan a Kano, Nasiru Salisu Zango ya wallafa a shafinsa na facebook, ya ce ɗansandan har masallaci ta gina a lokacin ya na shugabancin caji-ofis na Bompai, wato DPO, a jihar Kano.
A cewar Zango, ko a lokacin yana DPO, Sanusi ya na kyautata wa masu laifi da ke tsare, inda har katifa ya saka a dakunan tsararrun don kyautata wa ga ɗan adam.
Ya kuma ƙara da cewa Sanusi mutum ne mai matuƙar kirki da taimakon al'umma kamar yadda addinin Musulunci ya koyar.
@Daily Nigeria Hausa