Anyi jàna'izar jami’in EFCC da aka kashe wanda 'yan yahoo ne dai suka kashe a bakin aikinsa.
Ganin jami’an EFCC ke da wuya sa ’Yan Yahoo ɗin suka buɗe musu wuta, suka kashe wani mai muƙamin Mataimakin Sufurtanda, suka jikkata wani da raunin harbi a yayin da sauran jami’an suka sha da ƙyar.
Masu damfara ta intanet, waɗanda aka fi sani da ’Yan Yahoo, sun karbe wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arziƙin Ƙasa (EFCC), har lahira a bakin aikinsa.
’Yan Yahoo sun kashe shi tare da jikkata wani abokin aikinsa ne a yayin da shi da tawagar jam’an EFCC suka kai samame a wata matattarar ɓata-garin a Jihar Anambra.
Trust Radio