Ba zan Taimaki Gwamnatin Shugaba Tinubu ba Kuma mutane masu kima ba za su taimaka masu ba -Sarki Sanusi Na II

 Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya ce ba zai taimaki wannan gwamnatin ta Shugaba Tinubu ba.


Sarkin ya bayyana haka ne a wajen taron tinawa da fitaccen lauyan nan dangwagwarmaya na Najeriya, Chief Gani Fawehinmi karo na 21 a Lagos.

Yace, zai iya yin bayani a kan 'yan wasu abubuwa game da abubuwan da Najeriya ke ciki da hasashen abin da zai iya faruwa da kuma yadda za a iya kaucewa hakan, to amma ya ce ba zai yi hakan ba, domin idan ya yi hakan zai taimake su, shi kuma ya ce ba zai taimake su ba.

Mai martaban ya ce, ya yanke shawara cewa ba zai yi magana a kan tattalin arziki ko sauye-sauyen da gwamnatin ke yi ba ko ma ya yi bayani a kan komai, ''saboda idan na yi bayani hakan, za taimaki gwamnatin, to amma ba na son in taimaki gwamnatin nan.''

Ya kara da cewa, ''Abokanaina ne, to amma idan ba sa yin abu kamar abokanai, ni ma ba zan dauke su kamar abokanai ba.''

''Ba ma su da mutane masu kima da za su zo su yi bayanin abin da suke yi ba. Ba zan taimaka ba,'' in ji shi.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org