CBN ya ci tarar biliyan 1.35 kan bankuna 9 saboda karancin kudi a ATM dinsu

Babban bankin Najeriya, CBN ya ci bankuna 9 tarar kuɗi Naira biliyan 1.35 saboda kin sanya isassun kuɗi a n'aurorin cirar kuɗi na ATM dinsu, inda aka ci ko wane banki tarar Naira miliyan 150. 

Kuma za a cire kuɗin ne kai tsaye a asusun ajiyar bankunan da ke CBN. 

Bankunan su ne; Fidelity Bank Plc, First Bank Plc, Keystone Bank Plc, Union Bank Plc, Globus Bank Plc, Providus Bank Plc, Zenith Bank Plc, United Bank for Africa Plc, da Sterling Bank Plc.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, mukaddashin daraktar sashen watsa labarai ta CBN, Mrs Hakama Sidi ta jaddadda cewa za a rika sanya isassun kuɗi a ATM.


Alfijir Radio

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org