ECOWAS za ta gudanar da bikin raya al’adu da bunƙasa abinci a Katsina

 Ƙungiyar bunƙasa tattalin arzikin Afrika (ECOWAS) za ta yi bikin raya al’adu da bunƙasa samar da abinci a Katsina.

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Bikin da aka sanya wa suna “Samar da bunƙasa al’adun ƙasashen Afrika” tuni gwamnatin Katsina ta amince da ɗaukan nauyin bikin.

Da yake jawabi lokacin da wakilan Ƙungiyar ECOWAS suka kai masa ziyara a ofishin sa gwamna Dikko Raɗɗa ya nuna jin daɗin sa da ƙungiyar ta zaɓi jihar Katsina a matsayar jihar da za su gudanar da bikin.


Ya bayyana cewa Jihar Katsina a matsayin jihar da ke samar da abinci da kayan lambu,”zamu yi maraba da baƙi daga cikin gida da wajen ƙasa akan wannan biki”gwamna Raɗɗa ya fadi haka.


Gwamnan yana mai tabbacin cewa shugaban hukumar tarihi da raya al’adu Dr Kabir Ali Masanawa zai kawo cigaba da sauye sauye wajan bikin raya al’adu,da zai zama wajen yawon buɗe ido.

Babban darakta na hukumar ECOWAS a fannin abinci da bunƙasa al’adu Jakada Felix Ihonre a jawabin sa ya nuna jin daɗin sa ga irin kyakkyawar tarbar da akai masa shi da tawagarsa.

Ya bayyana cewa irin wannan biki zai kawo masu zuba hannun jari a fannin noma daga ciki da wajen ƙasar nan.

Ihonre ya bayyana hukumar raya al’adu na Jihar Katsina a matsayar mazaunin da yayi daidai da gudanar da bikin.


Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org